Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Wata babbar kotu da ke jihar Rivers ta yanke wa wani mutum mai suna Charles Baridolee hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same shi da laifin kashe wani mutum mai suna Gerald Tekena a shekarar 2024.

An tabbatar da cewa Baridolee ya kashe Tekena ne a kauyen Bodo da ke ƙaramar hukumar Gokana, bayan ya masa raunuka masu yawa da adda lokacin da suka yi faɗa.

Rahotanni sun nuna cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya kai wa marigayin hari ne saboda ya gargaɗe shi da ya daina ba wa iyalansa kuɗi, yana mai cewa hakan ne ya sa suka daina girmama shi a gida.

A lokacin da ake yanke hukunci ranar Alhamis, alkalin shari’ar, Mai Shari’a Augusta Chukwu, ta ce lauyoyin gwamnati sun tabbatar da zargin da suka gabatar da hujjoji da kuma furucin wanda ake tuhuma da ke tabbatar da aikata laifin.

A cewar alkalin, “Kotu ta gamsu cewa an tabbatar da laifin kisa ba tare da wata shakka ba, don haka wanda ake tuhuma, Charles Baridolee, ya kamata a rataye shi ta wuya har sai an tabbatar da mutuwarsa.”

Bayan kammala hukuncin, Ordu Precious, babban lauya mai gabatar da ƙara daga ma’aikatar shari’a ta jihar Rivers, ya ce hukuncin ya dawo da fata ga iyalan wanda aka kashe, tare da nuna cewa kotu har yanzu ita ce mafakar talakawa wajen neman adalci.

More from this stream

Recomended