Kotu ta yanke wa ɗansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin kisa kan zargin kisan kai.

Kotun da ke karkashin Mai shari’a C. D. Diai ta yanke wa Sufeton hukuncin kisa bisa laifin kashe wani dillalin waya, Mista Onyeka Ibeh, a Asaba.

Ibeh, wani shahararren dillalin waya a Asaba, tare da matarsa yana tuki ne daga Ugbolu zuwa Asaba a ranar 5 ga Afrilu, 2023, lokacin da rundunar ‘yan sanda suoa tare su domin bincike.

An ce marigayin ya tsaya amma bayan ya dau lokaci ana bincike, kuma ba a je wurinsu ba, sai ya yanke shawarar komawa gida.

Cikin fushi da matakin da mamacin ya dauka na juyawa, nan take sifeton ‘yan sandan ya budewa motar wuta, harsashin ya shige kan marigayi Ibeh kuma nan take ya mutu.

Sai dai matar marigayin da take zauna a kujerar gaba ba ta ji rauni ba.

More from this stream

Recomended