Kotu ta tura wata mata gidan yari bayan da ta ci zarafin wata ƴar sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta gurfanar da wata a gaban kotu mai suna, Omorogbe Jennifer Soni bayan da aka ɗauki hoton bidiyonta tana cin zarafin wata ƴarsanda.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Benjamin Hundeyin Shi ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata 27 ga watan Faburairu.

A cewar Hundeyin an tura Omorogbe ya zuwa gidan yarin Ƙiriƙiri kafin a cigaba da sauraron ƙarar a cikin watan Maris.

An gurfanar da matar ne a gaban kotun majistire ta Eti-Osa  dake Ajah.

Hundeyin ya yi kira ga mazauna birnin na Lagos da su kasance masu bin doka da oda.

More from this stream

Recomended