Kotun ɗaukaka ƙara dake Lagos ta tabbatar da hukuncin kisa akan Peter Nielsen wani ɗan ƙasar Denmark kan kisan matarsa da kuma ƴarsa.
A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a kotun ɗaukaka ƙarar tayi watsi da ɗaukaka ƙarar da Nielsen ya yi saboda rashin gamsassun hujjoji.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce gwamnatin jihar Lagos da ta shigar da ƙarar ta gabatar da ƙwararan hujjoji da suke tabbatar da cewa wanda ake zargin ya aikata laifin na kisan kai.
A ranar 13 ga watan Yuni ne na shekarar 2018 gwamnatin Lagos ta shigar da ƙarar Nielsen gaban babbar kotun jihar inda aka yi masa tuhume-tuhume biyu da suka shafi kisan kai.
Laifin ya saɓa da sashe na 223 na kundin dokar manyan laifuka ta jihar Lagos na shekarar 2015.
Ya kashe matarsa mai suna Zainab wacce aka fi sani da Alizee da kuma ƴarsu mai shekaru 3 a ranar 5 ga watan Afrilu na shekarar 2018 a gidansu dake unguwar Banana Island.