Kotu ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyar NNPP na jihar Kano

Wata babbar kotu dake jihar Kano ta sake tabbatar da dakatarwar da aka yiwa dakattacen shugaban jam’iyar NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa da wasu yan jam’iyar daga mazabarsa ta Gargari a karamar hukumar Dawakin Tofa su ka yi

A ranar 30 ga watan Disamba ne shugabannin mazabar ta Gargari suka kora tare da fatattakar Dungurawa daga shugancin jam’iyar na jiha, kasa da makonni biyu bayan sake zabarsa a matsayin shugaban jam’iyar.

Shugabannin mazabar su 27 ne suka cimma matsayar dakatar da Dungurawa bayan da suka zarge shi da da haddasa rikicin cikin gida a jam’iyar da kawo rabuwar kai.

Bayan cire shi daga kan mukaminsa ne aka naÉ—a, Abdullahi Abiya a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

A wata kara dake buÆ™atar kulawar gaggawa da Shuaibu Hassan da wasu mutane 9 suka shigar kotu,  kotun ta hana Dungurawa ayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyar NNPP na Kano har sai ta kammala sauraren Æ™arar.

More from this stream

Recomended