Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang ya nufi kotun koli domin neman hakkinsa bayan kotun daukaka kara ta ƙwace kujerar gwamna daga hannunsa.
Idan ba a manta ba kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Lahadi ne ta kori gwamnan jihar Filato, Mutfwang Manasseh na jam’iyyar PDP.
Ta kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, da ta amince da Nentawe Goshwe na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a matsayin zababben gwamna a zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Mai shari’a Elfrieda Williams-Dawodu, wadda ya jagoranci kwamitin mutum uku a lokacin da take yanke hukunci, ya buga misali da sashe na 177 na kundin tsarin mulkin kasar, inda ya ce Manasseh ba dan takara ne da PDP ta dauki nauyinsa ba a lokacin zaben.