Kotu ta samu shugaban rikon karamar hukuma da laifin satar Naira miliyan 54

Babbar kotun tarayya dake jihar Kebbi ta yankewa, Abubakar Bawa Makuku  shugaban riko na karamar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi hukuncin daurin shekaru  hudu ko kuma tarar miliyan 1 da kuma wata karin tarar miliyan 1.5 zai biya ƙaramar hukumar Sakaba a matsayin diya

Kotun ta samu shugaban da aikata laifin almundahana da kuma almubazzarancin kudaden kwangila har naira miliyan 54.

Hukumar ICPC dake yaki da hana cin hanci da karbar rashawa dama sauran laifuffukan da suka danganci haka ce ta gurfanar da shi a gaban kotun

Har ila yau kotun ta yankewa, Ahmed Abdullahi Fakai daraktan kuɗi na karamar hukumar hukuncin daurin shekaru  uku ko kuma tarar naira miliyan 2.5.

An gurfanar da mutanen biyu ne a gaban alkalin kotun mai shari’a, E. Gakko.

Tun da farko mutanen biyu sun musalta zargin da ake musu.

More from this stream

Recomended