Babbar kotun shari’ar musulunci ta jihar Kano ta ce ta samu Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara da dukkan laifukan da ake tuhumar sa.
Daga cikin tuhumar da ake masa, hadda zargin wa’azinsa zai iya tayar da tarzoma a jihar Kano.
Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya dage zaman don bashi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.
Sai dai kafin a tafi hutun Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya yi magana ta karshe inda ya ce lauyan da ke kareshi bai san shi ba kuma baya neman afuwa saboda a cewarsa bai aikata laifi ba, don haka a gaggauta yanke masa hukunci.
A ranar Juma’a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.