Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta kori,Yakubu Dogara daga kan kujerarsa inda ta ayyana kujerar a matsayin wacce babu kowa akai.
Dogara wanda yake wakiltar kananan hukumomin Dass/Bogoro a majalisar ta wakilai ta tarayya ya kasance shugaban majalisar daga shekarar 2015-2019.
Da yake yanke hukuncin alkalin kotun a yau ranar Juma’a mai shari’a,D.U Okorowo ya ce ya sauya shekar da Dogara yayi daga PDP zuwa APC ya saɓa doka saboda haka dole ya bar kujerarsa a majalisar.
Dogara ya sauya shekar ne bayan da suka samu sabani da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad.