Kotu Ta Ki Bayar Da Belin Tukur Mamu

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja taki yarda ta bayar da belin, Tukur Mamu mamallakin kamfanin jaridar Desert Herald.

Ana zargin Mamu da karbar kuÉ—in fansa har dalar Amurka 120,000 a madadin kungiyar yan ta’addar Boko Haram.

KuÉ—in ya karbe su ne daga wasu daga cikin iyalan fasinjojin jirgin kasar Abuja-Kaduna da aka yi garkuwa da su.

Tun a ranar 21 ga watan Maris ofishin Antoni Janar ya gurfanar da shi a gaban kotu inda ake masa tuhumarsa da aikata laifuka 10 da suka shafi ta’addanci.

Amma kuma Mamu ya musalta dukkanin zargin da ake masa.

Lauyan Mamu Sani Katu ya nemi kotun ta bayar da belin sa saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

Amma masu gabatar da kara sun nuna adawar su da buƙatar haka.

Da yake yanke hukunci kan bukatar a ranar Alhamis mai shari’a,Inyang Ekwo ya ce wanda ake zargi sun gaza bayan da gamsassun hujjoji.

Alkalin ya ce tun da hukumar dake tsare da Mamu sun nuna za su iya kula da shi kan rashin lafiyar da aka ce yana fama da ita to babu dalilin da zai sa ya bayar da umarnin belin.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...