Kotu ta ki amincewa da bukatar Yahaya Bello ta  zuwa ganin likita kasar waje

Wata  babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta ki yarda da bukatar da Yahaya Bello tsohon gwamnan jihar Kogi ya gabatar gabanta inda ya nemi ta amince masa ya tafi kasar waje domin a duba lafiyarsa.

A hukuncin da ya zartar ranar Litinin,alkalin da ya jagoranci zaman shari’ar, Emeka Nwite ya lura cewa rahoton likita dake hade da bukatar da aka gabatar masa baya dauke da sahannun likitan da ya wallafa shi.

Bello na fuskantar tuhume-tuhume 19 na zargin aikata almundahanar kudade da yawansu ya kai biliyan 80.2

Da yake gabatar da bukatar mai dauke da kwanan watan 20 ga watan Yuni, Joseph Daudu lauyan Yahaya Bello  ya ce likitan zuciya ne ya tura Bello zuwa wani asibiti a kasar Birtaniya. Inda ya kara da cewa a shekaru 8 da ya shafe yana jagorantar jihar Kogi bai taba fita zuwa wata kasar waje ba.

Daudu ya gabatar da sheda ta A da B dake dauke da rahoton kwararru kan lafiyar mutumin da yake karewa.

Ya ce Bello ya yi alkawarin tafiya ya dawo dai-dai lokacin da kotun take hutun shekara domin a cigaba da sauraren karar.

More from this stream

Recomended