Kotu ta hana VIO kamawa, tsare motoci ko cin tarar direbobi a kan hanya

Justis Evelyn Maha ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa, wanda aka fi sani da VIO daga tsayarwa, kwace, ko kama motocin da ke kan hanya.

Kotun ta kuma hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawan daga kakabawa direbobi tara.

Hukuncin da aka yanke a ranar 2 ga Oktoba ta hannun Justis Maha ya samo asali ne daga karar kare hakkin dan Adam da wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam kuma lauya mai kare muradun jama’a, Abubakar Marshal, ya shigar.

A cikin hukuncin, Justis Maha ta amince da hujjojin da mai shigar da kara ya gabatar cewa babu wata doka da ta ba da izini ga VIO da jami’anta su tsayar, kwace, ko kama motoci ko kuma su kakaba wa direbobi tara.

More News

TCN na ci gaba da ƙoƙarin gyaran wutar lantarkin da ta lalace kwana biyu

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da ci gaban da aka samu wajen farfado da rukunin wutar kasa bayan wata tangardar...

Magoya bayan jam’iyyar NNPP sun Æ™ona jar hula

Wasu daga cikin mambobin wani tsagi na jam'iyar NNPP sun barranta kansu da jagoran jam'iyar na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso inda suka riƙa...

PDP ta É—auki hanyar warware rikicin jam’iyyar

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ce  an kawo karshen rikicin cikin gida da ya dabaibaye jami'yar PDP. Mohammed wanda shi ne shugaban Æ™ungiyar gwamnonin...

Dakarun Najeriya sun cafke wasu Æ´an’aiken Æ´anbindiga a Kaduna

Sojoji sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da kaiwa 'yan bindiga sakonninsu a kasuwar ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia a...