Kotu ta hana likitoci tsunduma yajin aiki

Kotun sauraren karar ma’aikata ta kasa dake Abuja ta bayar da wani umarnin wucin gadi da ya hana mambobin kungiyar NARD ta  likitoci masu neman kwarewa shiga kowane irin yajin aiki.

E.D Subilim alkalin kotun ma’aikatan shi ne ya bayar da hukuncin umarnin a ranar Juma’a bayan  buƙatar gaggawa da gwamnatin tarayya ta shigar gabanta ta hannun,Lateef Fagbemi ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.

Gwamnatin tarayya ta shigar da karar kungiyar ta NARD,  Mohammad Usman Sulaiman shugaban kungiyar na kasa da kuma Shuaibu Ibrahim sakataren kungiyar na kasa.

Kungiyar ta sanar da cewa mambobinta za su tsunduma yajin aiki a ranar Litinin ga 12 watan Janairu a matsayin martani kan gazawar da gwamnatin tayi na  biyan buƙatun kungiyar da suka shafi kula da marasa lafiya dama dama walwalar likitocin.


Amma kuma a hukuncin da kotun ta yanke  alkalin kotun ya ce kotun ta gamsu da cewa bukatar da aka gabatar mata ta cika dukkan wasu sharuda duba da irin takaddun hujjojin dake hade da takardar neman bukatar.

Sublime ya ce umarnin zai cigaba da aiki har ya zuwa ranar 21 ga watan Janairu lokacin da kotun za ta saurari karar.
.

More from this stream

Recomended