Kotu ta bayar da umarnin  gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar Osun

Babbar kotun jihar Osun dake Osogbo ta bawa hukumar zaɓen jihar umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar a ranar Asabar.

Adeyinka Aderigbibge  alƙalin kotun shi ne ya bayar da umarnin a ranar Juma’a biyo bayan ƙarar da jam’iyar PDP ta kai hukumar zaɓen jihar a gaban kotun.

Aderigbibge ya kuma umarci jami’an tsaro da su samar da tsaro a zaɓen da za a gudanar na ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu.

Tun da farko gabanin hukuncin kotun gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya dage cewa za a gudanar da zaɓen da aka shirya gudanarwa duk da cewa babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi ya bada shawarar kada a gudanar da zaɓen.

A ranar Alhamis ne ya ce dole ne a mayar da shugabannin ƙananan hukumomin da aka sauke kamar yadda hukuncin kotun daukaka kara ya bayyana.

More from this stream

Recomended