Babbar kotun tarayya dake zamanta a Maitama a Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku kan kuɗi naira miliyan 150.
A ranar Litinin ne aka gurfanar da Ishaku gaban kotun tare da tsohon babban sakataren hukumar dake kula da ƙananan hukumomi da kuma masarautu ta jihar.
Dukkanin mutanen biyu ana masu tuhume-tuhume 15 da suka haɗa da haɗa baki wajen aikata zamba da kuma mallakawa kansu dukiyar al’umma.
Sun ƙi yarda sun amsa laifinsu bayan da aka karanta musu tuhume-tuhumen da ake musu.
A yayin zaman kotun na ranar Alhamis lauyoyin waɗanda ake ƙara sun gabatarwa da kotun buƙatar neman beli.
Lauyan hukumar EFCC Rotimi Jacob ya ce ba zai soki buƙatar bayar da belin ba.
Mai shari’a, Sylvanus Orji dake sauraron shari’a ya amince da buƙatar belin bisa wasu sharuɗa da ya gindaya.