
Wata babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta bawa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello izinin tafiya aikin Umrah a kasar Saudiyya.
Emeka Nwite alkalin da ya jagoranci zaman kotun shi ne ya amince da bukatar da babban lauya, Joseph Daudu ya gabatar gabansa a madadin, Bello.
Daudu ya ce buƙatar da ya shigar a ranar 20 ga watan Janairu ta bukaci a bayar da umarni na bayar da fasfon tafiye-tafiye na tsohon gwamnan domin ya samu gudanar da aikin Umrah.
Ya ce tsohon gwamnan na son ya yi kwanakin goman karshe na watan azumin Ramadan a kasar Saudiyya inda ya ce ana saka ran za a fara azumin watan ranar 18 ga watan Fabrairu a kuma kammala ranar 19 ga watan Maris.
Kemi Pinheiro lauyan hukumar EFCC ya gaza sukan bukatar da Bello ya nema.
Da aka tambaye shi da yayi karin haske kan tafiyar tasa Bello ya ce duk da cewa zai so a ce ya yi baki ɗayan azumin Ramadan a Makkah amma sanin cewa yana fuskantar shari’a yasa shi zabar yin kwanaki goma kaɗai.
Bello na fuskantar shari’a ne a gaban kotu inda ake tuhumarsa da almundahanar kudade da yawansu ya haura naira biliyan 80.

