Kotu ta sahalewa gwamnatin tarayya da ta kwace wasu jiragen ruwa guda biyu da aka samu da ɗaukar ɗanyen man fetur na sata a yankin Niger Delta.
A ranar 20 ga watan Janairu ne aka kama jirgin ruwa ma suna MT Kali a lokacin da yake satar mai a rijiyar mai ta Pennington mallakin kamfanin Shell dake jihar Bayelsa.
Kamfanin Tantita Security Services da gwamnatin tarayya ta ɗauka domin hana satar mai a yankin Niger Delta shi ne ya kama jirgin mai ɗauke da ma’aikata 20.
Har ila yau a cikin watan Faburairu aka kama jirgin ruwa mai suna MT Harbor da kuma Spirit lokacin da yake satar mai a rijiyar mai ta Sengana dake gaɓar ruwan jihar Bayelsa.
Ofishin Babban Sifetan Ƴan Sandan Najeriya,Kayode Egbetokun ne ya shigar da ƙara a gaban kotu.
Mai shari’a, J.K Omotosho alƙalin babbar kotun tarayya dake Abuja ya bayar da umarni da gwamnatin tarayya ta ƙwace jiragen MT Harbor da Sprit da abun da suke ɗauke da shi na wucin gadi.
Alƙalin ya umarci gwamnatin tarayya da ta dakata har tsawon makonni shida ko wani zai iya zuwa ya bayyana dalilin da zai sa ba za a ƙwace jiragen ba.