Kotu ta bawa gwamnatin tarayya damar ƙwace wasu jiragen ruwa dake satar mai

Kotu ta sahalewa gwamnatin tarayya da ta kwace wasu jiragen ruwa guda biyu da aka samu da É—aukar É—anyen man fetur na sata a yankin Niger Delta.

A ranar 20 ga watan Janairu ne aka kama jirgin ruwa ma suna MT Kali a lokacin da yake satar mai a rijiyar mai ta Pennington mallakin kamfanin Shell dake jihar Bayelsa.

Kamfanin Tantita Security Services da gwamnatin tarayya ta É—auka domin hana satar mai a yankin Niger Delta shi ne ya kama jirgin mai É—auke da ma’aikata 20.

Har ila yau a cikin watan Faburairu aka kama jirgin ruwa mai suna MT Harbor da kuma Spirit lokacin da yake satar mai a rijiyar mai ta Sengana dake gaɓar ruwan jihar Bayelsa.

Ofishin Babban Sifetan Ƴan Sandan Najeriya,Kayode Egbetokun ne ya shigar da ƙara a gaban kotu.

Mai shari’a,  J.K Omotosho alÆ™alin babbar kotun tarayya dake Abuja ya bayar da umarni da gwamnatin tarayya ta Æ™wace jiragen MT Harbor da Sprit da abun da suke É—auke da shi na wucin gadi.

Alƙalin ya umarci gwamnatin tarayya da ta dakata  har tsawon makonni shida ko wani zai iya zuwa ya bayyana dalilin da zai sa ba za a ƙwace jiragen ba.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum É—aya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe Æ´an ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faÉ—a tsakanin Æ´anbindiga da Æ´anbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...