Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bada umarnin a cigaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a hannun hukumar EFCC.
A ranar Laraba, aka gurfanar da Bello da kuma sauran waɗanda ake tuhumarsa tare Omar Shoaib Oricha da kuma Abdulsalami Hudu a gaban kotun inda ake tuhumarsu da aikata laifuka 16 dake da alaƙa da al-mundahanar kuɗaɗe.
Tsohon gwamnan ya musalta aikata laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.
Bayan an gama gurfanar da su lauyan Yahaya Bello, Joseph Daudu ya gabatarwa da kotun buƙatar a bashi belin wanda yake karewa.
Amma Kemi Pinheiro lauyan EFCC ya nuna adawarsa da buƙatar neman belin.
Bayan musayar yawu da zafafan kalamai a tsakanin lauyoyin a ƙarshe alƙaliyar kotun, mai Shari’a, Maryann Anenih ta ce hukumar EFCC ta cigaba da tsare Bello da sauran mutanen har ya zuwa ranar 10 ga watan Disamba.