Kotu ta bada belin waɗanda suka shirya auren jinsi

Wata babbar kotu dake zamanta Effurun karamar hukumar Uvwie ta jihar Delta ta bayar da belin mutane 69 da ake zargi da hannu a shirya auren jinsi.

Lauyan wadanda ake zargi, Mr Ochikwo Ohimor shi ne ya bayyana haka ga manema labarai da yammacin ranar Talata.

Ya ce an bayar da belin waɗanda ake zargi kan kuɗi N500, 000 da kuma mutane biyu da za su tsayawa kowanennsu.

“Waɗanda za su tsaya musunm dole su kasance suna zaune a yankin Effurun inda aka gurfanar da su a cikin watan Agusta.”

A ranar 27 ga watan Agusta ne yan sanda suka kama mutanen a lokaci da suke tsaka da gudanar da bikin auren jinsi.

More News

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...

Sojojin Najeriya Sun Musanta Jita-jitar Mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Daga Sabiu AbdullahiRundunar Sojojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja,...