Kotu ta aike da Danbilki Kwamanda gidan yari

Kwamanda lokacin da yake fitowa daga kotu

Wata kotun majistire dake zamanta a Nomansland jihar Kano ta tura, Abdulmajid Danbilki Kwamanda ya zuwa gidan yari.

Alkalin kotun mai shari’a, Aminu Magashi shi ne ya zartar da hukuncin bayan da aka gurfanar da Kwamanda a gabansa.

Ana zargin sa da aikata laifuka uku ciki har da zargin bata sunan gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

A cikin wata hira da yayi a gidan wani rediyo mai zaman kansa Kwamanda ya zargi Ganduje da bai wa shugaban kwamitin riko na jam’iyar APC, Mai Mala Buni kudi domin ya rantsar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyar na Kano

More from this stream

Recomended