Ko sanya tabaran likita na bata ma ido?

[ad_1]

Hakkin mallakar hoto
AFP

Mutane da dama sun yi amanna cewa idan ka dade kana amfani da tabaran likita karfin idonka zai ci gaba da raguwa maimakon ya karu.

A takaice a nan mutane da dama sun yarda cewa amfani da gilashin likita(Medikal) ba ya sa idon mutum ya gyaru yadda zai daina amfani da shi sai dai ya zama ma ba abin da mutum zai iya sai da shi a can gaba.

Claudy Hammond ta bincika mana wannan lamari.

Akwai dalilai da dsama da suka sa mutane ba sa son sanya tabaransu na likita.

Wadansu saboda suna ganin ba ya musu kyau, za a iya yi musu dariya idan suka sanya shi, wasu kuma sun fi jin dadi idan ba su sa shi ba.

Bayan jin dadi da ado, wasu mutanen kuma sun ganin yawan sa shi zai sa su dogara da shi ko da yaushe,ta yadda zai da shi za su iya gani da kyau.

Wani bincike da aka gudanar a Najeriya a shekara ta 2013 ya nuna cewa dalibai kashi 64 cikin dari sun yi amanna sanya tabaran likita na iya bata idanuwa.

A jihar Karnataka ta Indiya kuwa daliban kashi 30 cikin dari ne suke ganin amfani da gilashin na bata ido, yayin da a Pakistan kuwa kashi 69 namutane ne suka yarda da hakan.

A Brazil kuwa hatta ma’aikatan lafiya ma sun yi imanin cewa amfani da tabaran kara ganin yana kara lalata ido ne, inda a sannu a sannu yake rage maka kwarin ido. Ko akwai wata shaida da ta tabbatar da gaskiyar wannan magana tasu?

Akwai larurar ido iri biyu da ke sa ana amfani da tabaran likita, daya ita ce wadda mutum ba ya iya ganin abin da yake nesa sosai (short-sightedness,myopia) da kuma wadda mutum ba ya iya ganin abin da yake kusa da kyau sai na nesa (long-sightedness,hyperopia).

Ita larura ta biyun wadda mutum ba ya ganin abin da yake kusa sosai tana da alaka ne da yawan shekaru.

Mutane da yawa daga shekara 40 zuwa 50 suke fara gamuwa da ita ta yadda ba sa iya karatu sosai a wurin da ba shi da haske sosai.

Ita wannan tana faruwa ne, ta yadda, idan muka fara manyanta kwayar idanunmu take kara kankamewa ko tauri, ba ta sauyawa ta yadda za ta rage girma ko kara girma yadda za ta zo daidai nisan da ido ya gano abu.

Idan mutum ya kai lokacin da ba ya iya karatu da kyau idan ya rike littafi a tsawon hannunsa ko kuma rubutun wayar salularsa ko wata takarda, to daga nan sai ya fara neman tabaran likita.

Abin mamaki a nan shi ne yadda ya kasance gwaje-gwajen da aka yi kan tasirin yawan amfani da tabaran kara ganin ba su da yawa.

Kuma daga abin da muka sani babu wata shaida tabbatacciya da ta nuna cewa yawan amfani da gilashin na kara rage karfin gani.

To idan haka ne me ya sa ke nan mutane da yawa ba tare da wani dalili na kimiyya ba suke ganin yawan amfani da tabaran ya kara bata musu idanu?

Mutane za su ga a hankali a hankali suna ci gaba da dogaro da gilashin ta yadda ba sa iya gani da kyau sai da shi, ba su san cewa saboda idon nasu na kara rauni ne ba saboda karin shekaru.

Sai kawai su dauka cewa ai tabaran ne ya kara lalata musu ido, inda kuma a zahirin gaskiya ba haka abin yake ba domin abu wata dangantaka tsakaninsu.

Ko kana amfani da gilashinka ko ba ka amfani da shi, hakan ba zai hana karfin idonka raguwa ba a can gaba ( ko da ike ma idan har kana tilastawa idonka wajen karatu za ka iya samun ciwon kai ko kuma idanuwanka su rika zafi).

To sai dai lamarin ya bambanta a wurin yara. Domin amfani da tabaran da bai dace ba ko kuma kin yin amfani da shi ma gaba daya idan har da bukatar hakan zai iya shafar idanuwan a can gaba.

A tsawon daruruwan shekaru ana ganin ba wa yaran da suke da larurar da ba sa iya ganin abu na nesa sosai tabaran da bai kai wanda ya kamata a ba su ba ka iya gyara musu wannan matsala idan suka jima suna amfani da shi.

Tunanin masana a wancan lokacin shi ne, idan aka bai wa yaro gilashin da ya dace da shi yana ganin abin da ke nesa da kyau, kwayar idonsa za ta rika kokarin kara tsawon kanta idan yana kallon abin da yake kusa domin ganinsa da kyau.

To amma wani gwaji da aka yi a Malaysia a 2002 ya nuna wannan dabara ba daidai take ba saboda haka aka dakatar da amfani da ita bayan shekara daya.

An tara wasu yara ne 94 masu larurar da ba sa iya ganin abu daga nesa da kyau inda aka ba wa wasunsu tabaran da ba zai gyra musu ganinsu ba da kyau saura kuma aka ba su wanda ya yi musu daidai.

Lokacin da aka fara gwajin yaran suna rukunin shekara tara ne zuwa 14.

Bayan shekara biyu da aka gwada su sai aka ga,sabanin abin da aka yarda da shi can a shekarun 1960, yaran da aka ba su tabaran da bai yi daidai da idanuwansu ba, maras karfi sosai, kwayar idonsu ta kara tsawo, ma’ana matsalarsu tana karuwa.

Hakkin mallakar hoto
Thinkstock

Image caption

A shekaru da dama wasu na ba wa yara tabaran da bai kai karfin wanda ya kamata a ba su ba, wanda sheda ta nuna hakan bai dace ba

Wasu na ganin duk da haka har yanzu babu wata sheda da za ta sa a dauki wata tartibiyar matsaya ko magana a kan wannan matsala.

Amma a wani nazari da kungiyar masu binciken kimiyyar lafiya ta duniya, Cochrane, ta yi a 2011 a kan hanyoyin yi wa yara wadanda ba sa ganin abin da ke nesa da kyau magani, ta ce, ‘yan takaitattun shedun da ake da su sun nuna cewa ya fi dacewa a bai wa yara tabaran da ya dace maimakon da sani a ba su wanda bai kai karfin wanda ya kamata ba.

Babu wata sheda da ke nuna cewa amfani da tabaran zai iya sa larurarsu ta karu a kan kin amfani da shi samsam.

Hasali ma sakamakon nazarin da aka yi kan karuwar cutar ta rashin gani daga nesa da kyau, mafi dadewa wanda kwanan nan aka bayyana sakamakonsa guda 23 ya nuna akasin hakan, wato idan ba a ba su tabaran sun yi amfani da shi ba, hakan ke kara larurar.

Can a shekara ta 1983 an gwada wasu tarin yara masu larurar rashin ganin abu daga nesa da kyau a Finland, inda aka jarraba su a yanayi daban-daban, ciki har da yin karatu ba tabaran likita.

An gano cewa larurar tasu ta rika karuwa da sauri fiye da ta wadanda suke amfani da tabarau a ko da yaushe.

Bayan shekaru uku na farkon binciken sai aka shawarci dukkaninsu su rika amfani da tabaransu a ko da yaushe. Bayan shekara 20 sai aka ga babu wani bambanci a tsakaninsu.

Saboda haka amfanin tabaran likita a wurinka idan kai yaro ne da ke bukatarsa, a bayyane yake.

Idanun yara na bukatar ya koyi gani ko kallo, saboda haka idab ba a ba yaro gilashin da ya dace ba, yaran zai iya samun abin da ake kira ragon idanu(lazy-eye) saboda kwayar idanuwansa ba ta saba da ganin siffa ko hoto tangaran ba.

Haka kuma an gano cewa amfani da wannan hanya da ta dace wajen yi wa yaro maganin larurar zai taimaka masa wajen karatu da hanzari da kuma kawar da hadarin idonsa ya zama wurkilili ko harara-garke.

To idan muka bar maganar yara muka koma kna ta manya kuwa, abin mamaki shi ne rashin binciken da aka yi a wannan fanni. Za mu yi tsammanin cewa kimiyya ta samar da duk bayanin da ake bukata a kai, amma abin takaicin sai ka ga ba a yi nazari a kan abin da ya kamata ace anyi ba.

Nazarin da aka yi wanda ya ce bai kamata yaran da ba sa iya ganin abin da ke nesa ba su yi amfani da tabaran likita, ya sabawa ka’ida saboda illar da aka gano na tattare da hakan kan ilimin yaran da kuma bunkasar idanuwansu.

Amma kuma duk ha haka kamata ya yi a ce an yi irin wannan bincike a kan manya su ma, wadanda suke da matsalar iya ganin abu na kusa da kuma wadanda ba sa iya ganin na nesa da kyau.

Saboda haka yanzu an bar mu da tambayar me ya sa ba wanda yake son gudanar da wannan bincike?

Farfesa Ananth Viswanathan, babban likita a asibitin ido na Moorfields da ke Landan, yana ganin abin da ya sa ba wani bincike a kai watakila shi ne saboda babu wata sheda da ta nuna a zahiri tabaran likita na iya bata ido.

Bincike ba kawai yana bukatar neman alakar wani abu da wani abu ne ba kawai kafin a yi shi, yana kuma son ganin akwai wani dan dalili da zai iya sa abu ya zama gaskiya.

Saboda haka irin wannan bincike ba abu ne da ake sa ran ganinsa ba a nan kusa, a don haka sai mu ci gaba da dogaro da abin da ake cewa jiki magayi.

Kuma duk da cewa akwai dalilan da ke hana wasu amfani da tabaran likita, tsoron cewa za ka bata idonka ba ya daya daga cikinsu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Does wearing glasses weaken your eyesight?

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...