Dan wasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, zai iya barin ƙungiyar idan kwantirginsa ya kare a lokacin bazara, inda Newcastle United ta shiga jerin masu sha’awarsa. (Express)
Dan wasan gaba na gefe na Chelsea Hakim Ziyech, dan Moroko mai shekara 28, da kuma dan gaban Jamus Timo Werner, mai shekara 25, sun kasance wadanda Barcelona za ta nema a madadin Raheem Sterling, na Manchester City, idan kungiyar ba ta samu nasarar janye dan Ingilar mai shekara 26 ba a watan Janairu. (ESPN)
Paris St-Germain ta yi watsi da bukatar farko da Manchester United ta gabatar kan kociyanta Mauricio Pochettino. (Manchester Evening News)
Tsohon kociyan Tottenham, Pochettino, mai shekara 49, sai ya jira akalla wata shida kafin ya kama aiki da United. (Star)
Manchester United din ta tattauna da tsohon kociyan Borussia Dortmund Lucien Favre da tsohon mai horas da Lyon Rudi Garcia kan aikin wucin-gadi. (Telegraph)
Wadanda kungiyar ta Old Trafford take zawarci da aikin na rikon kwarya har da tsohon kociyan RB Leipzig Ralf Rangnick da tsohon kociyan Roma Paulo Fonseca. (Mail)
A cire wani zane na hoton kociyan United da aka kora Ole Gunnar Solskjaer daga Old Trafford. (Sun)
Liverpool da Barcelona na sha’awar dan gaban Chelsea Christian Pulisic, mai shekara 23, amma kuma Blues ba za ta sayar da shi ga wata kungiya abokiyar hamayyarta ba a Premier, kuma ita Barcelona ba ta da yuro miliyan 50 da za ta sayi dan wasan gaban na gefe dan Amurka. (El Nacional)
Chelsea ta tattauna da dan bayan Fenerbahce da Hungary Attila Szalai, mai shekara 23. (Football Insider)
Wolves za ta saurari masu bukatar sayen dan gabanta na gefe dan Sifaniya Adama Traore, mai shekara 25, a watan Janairu. (Football Insider)
Wakilin Gareth Bale, Jonathan Barnett ya ce magoya bayan Real Madrid sun takura wa dan gaban na Wales. Kwantiragin Bale, mai shekara 32, da Rel Madrid na nan har zuwa bazara ta gaba. (Marca)
Kungiyoyin da suka hada da Atletico Madrid da Barcelona da Newcastle da kuma AC Milan na bin diddigin dan gaban Arsenal da Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 30, wanda kwantirginsa zai kare a bazara. (Calciomercato)
Gunners din su kuma suna sha’awar sayen dan wasan tsakiya na Lille dan Portugal Renato Sanches, mai shekara 24, a watan Janairu. (Football London)
Har yanzu dan wasan gaba na Ingila da Manchester United Jesse Lingard, mai shekar 28, yana son barin United duk da tafiyar Solskjaer daga Old Trafford. (Star)
Newcastle na shrin gogayya da Manchester United wajen sayen dan bayan Atletico Madrid dan Ingila Kieran Trippier, mai shekara 31. (Sun)
Norwich City na son tsohon dan tawagar ‘yan kasa da shekara0 ta Ingila Keinan Davis na Aston Villa mai shekara 23. (Football Insider)
Kila kociyan Newcastle Eddie Howe, mai shekara 43, ya jagoranci sabuwar kungiyar tasa a karawarta da Arsenal ranar Asabar duk da cew y kamu da Korona a makon da ya gabata. (Mail)