Connect with us

Hausa

Kasuwar cinikin ƴan ƙwallo: Ronaldo da Messi da Haaland da Coman da Donnarumma da Jorginho

Published

on

Lionel Messi

—BBC Hausa

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 36 idan ya yanke shawarar barin kulob ɗinsa. (Le Parisien – in French)

Ɗan wasan gaba na Argentina Lionel Messi mai shekara 33 zai buga wasa a kakar wasa biyu a Turai kafin komawa Inter Miami. (Cadena Ser – in Spanish)

Chelsea na zawarcin ɗan wasan Bayern Munich Kingsley Coman mai shekara 24 a matsayin wanda zai maye gurbin Christian Pulisic, idan ɗan wasan na Amurka mai shekara 22 ya nuna sha’awar son barin Stamford Bridge. (Mail)

Arsenal da West Ham da Everton da Brighton na tattaunawa kan sayen ɗan wasan Scotland ɗan shekara 18, Ibane Bowat daga Fulham. (TeamTalk)

Ɗan wasan tsakiya na Manchester United Nemanja Matic mai shekara 32 ya ce zai duba yiwuwar komawa Benfica idan har aka tuntuɓe shi duk da cewa ɗan wasan na Serbia ya dage cewa yana jin daɗin kasancewarsa a Old Trafford. (Sport TV, via Sun)

Barcelona ta yi tayin sayen Georginio Wijnaldum, dan wasan tsakiya na Netherlands mai shekara 30 wanda ake sa ran zai bar Liverpool idan kwantiraginsa ya ƙare a ƙarshen wannan kakar wasan. (Football Insider)

Inter Milan ma ta tattauna da wakilin Wijnaldum amma an samu tsaiko yayin da kulob ɗin ke duba wasu ƴan wasan. (Calciomercato – in Italian)

Tsohon kocin Chelsea Maurizio Sarri na shirin komawa Napoli a matsayin koci, lamarin da ka iya sa ɗan wasan tsakiya na Chelsea ɗin Jorginho shima ya koma kungiyar ta Italiya. (Radio Kiss Kiss, via Express)

Ita ma Juventus ta nuna sha’awar sayen Jorginho ɗan Italiya mai shekara 29 . (Tuttosport – in Italian)

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending