
Shugaban Faransa Emmanuel Macron lokacin da ya halarci wurin da lamarin ya faru
Nan gaba a yau, a ke sa ran shugabannin kasashen duniya za su gudanar da wani taron tattaunawa da manufar nemawa Lebanon tallafi, kwanaki biyar bayan fashewar da ta janyo gagarumar asarar rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shugaban Farasa Emmanuel Macron, da takwaransa na Amurka Donald Trump na cikin shugabannin da za su albarkaci taron wanda Faransa da Majalisar dinkin duniya su ka shirya gudanarwa ta bidiyon kai tsaye.
Mahukunta sun yi kiyasin cewa asarar da fashewar ta haifar ta haura ta Dalar Amurka biliyan goma sha biyar.
Sannan lamarin ya janyo mutuwar mutum 158, kana wasu 5000 sun mutu, sai kuma mutum 3000 da suka rasa matsugunansu.
Yadda lamarin ya fusata jama’a.
Dandazon mutane da suka taru suna zanga zanga sakamakon fusata su da lamarin ya yi
Ranar Asabar ‘yan kasar da dama sun kwarara a kan tituna, yayin da wasu rahotanni ke cewa sun rika fasa gine-ginen gwamnati, da cillawa yan sanda duwatsu da abubuwan fashewa.
Sai dai yayin wani jawabi ta kafar talabijin din kasar. Frai ministan Lebanon Hassan Diab, ya lallashi jama’a, tare da yin kiran gudanar da zabe tun kafin lokacin yin shi ya zo, ya na cewa ta haka ne za a iya magance matsalolin da suka kunno kai.
Dama dai kasar na cikin matsaloli kamar mashashsharar tattalin arziki, da annobar korona, baya ga rashin aiki a tsakanin yi.
Ko da a watan Octoban da ya gabata, ‘yan kasar sun gudanar da zanga-zanga, suna kiran gwamnati ta magance matsalardurkushewar darajar kudin kasa.
Mahukunta sun ɗora alhakin fashewara kan tan 2,750 na sinadarin ammonium nitrate da aka jibge cikin wani ɗakin ajiyar kaya na tashar jirgin ruwan birnin.
Mene ne sanadin fashewar ?
Shugaban Lebanon Michel Aoun ya ɗora alhakin fashewar tan 2,750 na sinadarin ammonium nitrate da aka jibge cikin wani ɗakin ajiyar kaya na tashar jirgin ruwan birnin.
A shekarar 2013, wani jirgin ruwa mai suna MV Rhosus yayi jigilar sinadarin. Bayan ya yada zango a tashar jirgin ruwa na Beirut saboda wata matsalar inji a kan hanyarsa daga ƙasar Georgia zuwa Mozambique, sai hukumomin tashar suka hana shi barin tashar bayan sun binciki kayan da yake ɗauke da su.
Kamar yadda shafin intanet na Shiparrested.com ya ruwaito, masu jirgin ruwan sun yi watsi da lamarin jirgin ruwan nasu a tashar, lamarin da yasa aka kwashe sinadarin daga ciki zuwa wani ɗakin ajiya mai lamba 12 bayan wata kotu ta bayar da umarnin yin haka.
Tun wancan lokacin sinadarin ke jibge cikin ɗakin, maimakon a sayar da shi ko dai a raba shi da wurin.
Wa ke da alhakin fashewar ?
Wasu bangarorin birnin Beirut da lamarin ya lalata
Shugaba Aoun ya yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike kan fashewar.
“Mun ƙuduri niyyar ci gaba da bincike kuma za mu bayyana yadda wannan abin takaicin ya auku ba tare da jinkiri ba, kuma duk wadanda aka samu da sakaci da ya janyo fashewar za su ɗandana kuɗarsu,” inji shugaban ranar Laraba bayan ya zaga cikin tashar jirgin ruwan.
Firai minista Hassan Diab ya bayyana yadda aka bari fasewar ta auku “abin da ba za a amince da shi ba.”
Shugaban hukumar kwastam na ƙasar, Badri Daher ya ce an yi watsi da kashedin da hukumar ta sha yi kan haɗarin ajiye sinadarin na lokaci mai tsawo.
“Mun buƙaci a sayar da shi ga masu buƙata a ƙasashen ƙetare amma aka kasa yin haka. Mun bar komai ga ƙwararru da masu ikon dubawa su bayyana abin da yasa haka ya faru,” kamar yadda Mista Daher ya sanar wa tashar talabijin ta LBCI mallakin gwamnatin ƙasar.
Shugaban Lebanon Michel Aoun ya ƙuduri aniyar hukunta wadanda aka samu da laifin fashewar
Gwamnatin Lebanon ta umarci da a tsare jami’an da ke da alhakin kula da wuraren adana kaya, musamman waɗanda ke kula da ɗakin da aka tara sinadarin ammonium nitrate din har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Ƴan ƙasar ta Lebanon da dama ba su gamsu da alƙawuran da gwamnatinsu ke yi ba na baza sakamakon binciken a faifai. Suna kallon binciken a matsayin wani yunkurin kaucewa ɗaukar alhaki a bangaren shugabannin siyasar ƙasar da tuni sunansu ya ɓaci saboda aikata cin hanci da rashawa da kuma rashin iya gudanar da albarkatun ƙasa.