Kasashen Afirka na taron zuba jari a Birtaniya | BBC Hausa

Boris Johnson

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Birtaniya ta gayyaci taron ne a daidai lokacin da ta ke gab da ficewa daga Tarayyar Turai

A ranar Litinin ne ake sa ran bude babban taron koli kan zuba jari tsakanin Birtaniya da nahiyar Afurka. Shugabanin kasashen Afrikar 21 ko wakilansu ne ake sa ran za su halarci taron wanda Firaminista Boris Johnson zai karbi bakuncinsa.

Za a yi wannan taro ne dai kasa da makonni biyu kafin kasar ta fice daga Tarayyar Turai wani abu da zai kawo sauyi ga manufofin cinikayyarta. Masana tattalin arziki sun ce wannan taro ya na da muhimmanci ga Birtaniya da za ta kara fadada harkokin kasuwanci da kasashen duniya.

Farfesa Muhamnmad Muttaqa Usman, masani kan harkokin tattalin arziki a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a Najeriya ya shaidawa BBC cewa ana gudanar da taron a kan gaba ne, idan aka lura da kokarin kasashen Afurka na samar da tasu kungiyar ta Tarayyar Afurka.

”Kasashen Afurka su na neman hada hancin cinikayyarsu ta hanyar amfani da Tarayyar Afurka, wanda zai zo daidai da abin da hadakar ke bukatar ganin an cimma kudurin da suke neman cimma daga nan zuwa shekarar 2063.

Shi daman tattalin arziki ba zai bunkasa ba sai ka na hulda da kasashe da yawa, wani abun dubawa shi ne yanzu China ta na da kyakkyawar alakar kasuwanci da kasashen Afurka wanda ya kai ana ganin tattalin arzikinta ya kai ma’aunin kashi 6 cikin 100 a wannan shekara wanda a baya bai kai haka bunkasa ba.”

Sai dai ana fargabar alakar da ke tsakanin Birtaniya da kasashen Afurka babu wani abin azo a gani da Afurkar ke mora, Farfesa ya ce idan kasashen furka kudu da sahara suka ci gaba da tafiya babu ci gaba, babu wutar lantarki, da ababen more rayuwa da cin hanci da rshawa da ya yi wa wasu daga ciki katutu tabbas Birtaniya ce za ta sha romon wanna alaka ta kasuwanci.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya na daga cikin shugabannin kasashen Afurka da ke halartar taron a Birtaniya, a daidai lokacin da gwamnatinsa yakin magance cin hanci da rashawa da masana sukai amanna da cewa ya na yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.

More News

Wani mutumi ya yi garkuwa tare da kashe Æ´ar’uwarsa a Kaduna

A ranar Lahadin ne mazauna birnin Zariya na jihar Kaduna suka shiga alhini cikin alhini sakamakon kama wani mai suna AbdulAzeez Idris da ake...

ÆŠan ta’addar Boko Haram ya miÆ™a kansa ga sojoji

Alhaji Wosai wani mamba a ƙungiyar ƴan ta'addar Boko Haram ya miƙa kansa ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai. Rahotanni sun bayyana...

An kuÉ“utar da wasu É—aliban da aka sace a jami’a a Kogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa an ceto 14 daga cikin daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence da ke Osara Okene...

Hukumar NMDPRA ta rufe wani gidan mai da ya karkatar da tankar man fetur 18

Hukumar NMDPRA dake lura da tacewa tare rarraba man fetur da iskar gas ta rufe gidan man Botoson Oil and Gas LTD dake jihar...