
Asalin hoton, Getty Images
Real Marid ta kai zagaye na biyu a gasar Champions League, bayan da ta yi nasara a kan Borussia Munchengladbach da ci 2-0.
Karim Benzema ya buga karawar kuma na 527 da ya yi wa Real Madrid, kuma hakan ya sa ya yi kan-kan da Roberto Carlos a wannan bajintar.
Dan wasan tawagar Faransa shi ne ya ci kwallaye biyun da ya kai Real Madrid wasan zagaye na biyu a wasannin bana.
Dan kwallon Brazil shi ne ya fara buga wasa 527, kuma dan wasa daga waje da ya buga karawa da yawa a Real Madrid.
Roberto Carlos ya yi wannan bajintar a kaka 11 a Santiago Bernabeu, ya kuma kofi 12.
Kakar 2020/21 ita ce ta 12 da Benzema dan kwallon Real Madrid ke taka leda a Real Madrid, tun bayan da ya koma Spaniya daga Lyon a 2009.
Marcelona shima ya taka rawar gani, inda ya buga wasa 515, wanda tuni Benzema ya haura shi tun shekarun baya.
Kuma Benzema shi ne na biyar a cin kwallayen da 257 a raga.
Cristiano Ronaldo shi ne na farko kan ci wa Madrid kwallaye da 451 a raga.
Wanda yake na biyu shi ne Raul da 323, sai Alfredo di Stefano da308 da kuma Santillana da ya ci 290.
(BBC Hausa)