Karim Benzema ya ci wa Real Madriid kwallo tara a wasa 11 da ya buga a gasar La Liga ta bana.
Dan wasan tawagar Faransa ya ci kwallo kaso 35 cikin 100 na yawan kwallo 26 da Real ta zura a raga a kakar bana kenan.
Hakan ne ya sa Benzema a kan gaba a kyautar takalmin zinare da ake bai wa wanda yafi yawan cin kwallaye da ake kira Pichichi a Sifaniya.
To sai dai kuma kawo yanzu Benzema na takara da Vinicius Junior wanda keda bakwai a raga.
Dan wasan tawagar Brazil yana da kaso 26 ciki dari a kwallo 26 da Real Madrid ta ci kawo yanzu kenan.
Ranar Asabar, Real Madrid ta doke Elche da ci 2-1 a wasan mako na 12 a gasar La Liga, kuma Vinicius Junior ne ya ci biyun.
A karon farko za a lashe takalmin zinare ba daga wajen Lionel Messi ba, wanda ya ci biyar a jere a Barcelona.
Messi wanda ya fara lashe kyautar a kakar 2008/09 yana da takwas jumulla kafin ya bar Barcelona a kakar nan.
A kakar da ta wuce Lionel Messi ya lashe kyautar Pichichi karo na biyar a jere, bayan da ya zura kwallo 30 a raga har da uku a bugun fenariti da barar da biyu.
Kyaftin din tawagar Argentina ya koma Paris St Germain dda taka leda a bana.
Jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga:
- K. Benzema R. Madrid 9
- V. Júnior R. Madrid 7
- L. Suarez Atletico 6
- M. Oyarzabal R. Sociedad 6
- R. d. Tomás Espanyol 6
- M. Depay Barcelona 5
- A. Danjuma Villarreal 5
- W. Jose R. Betis 4
- Juanmi R. Betis 4
- C. Soler Valencia 4
(BBCHAUSA)