Karatu a Cyprus ta Arewa: Ana ce-ce ku-ce kan tafiya karatu kasar waje

Kasashen duniya basu amince da Cyprus ta Arewa ba
Bayanan hoto,
Kasashen duniya basu amince da Cyprus ta Arewa a matsayin kasa ba

Zargin hallaka dalibai ‘yan Najeriya da ake tura wa karatu Cyprus ta Arewa ya kasance abin da ‘yan ƙasar ke tafka muhawara a kai da ba da bahasi a shafukan sada zumunta.

Wannan na zuwa ne bayan Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje Abike Dabiri-Erewa ta gargadi iyaye kan tura ‘ya’yansu ƙasar don karatu.

Miss Abike ta yi wannan gargadin ne bayan Hon. Justice Amina Ahmed Bello, mahaifiyar wani dalibi da ya mutu a yankin ta kai mata koke.

Mutuwar dalibi Ibrahim Khaleel da ke karantun Injiniya, wanda kuma ake zargin kashe shi aka yi a kasar ya sake bayyana irin hadarin da ake gani ‘yan Najeriya ke ciki a wannan kasa.

Abike ta jadada cewa mutuwar Khaleel, wanda ke zango na uku na karantun Injiya, ta sake fito da hali da bankado da yada ake kashe ‘yan Najeriya babu ƙaƙƙautawa a Cyprus ta Arewa ba tare da sanin dalili ba.

Hukumar da Abike ke shugabanta ta ce sama da ‘yan Najeriya 100 aka kashe Cyprus ta Arewa, wanda abin damuwa ne sosai, sai dai kokarin tura wakilai ko tattaunawar diflomasiya domin bincike abu ne mai wahala saboda yankin ana masa kallon wani bangare ne na kasar Turkiyya.

Abin da mutane ke cewa a Twitter

Tun bayan fitar da gargadin hukumar, ‘yan Najeriya mazaunan ƙasashen ƙetare, da sauran ‘yan ƙasar da dama ke ta mayar da martani musamman a shafukan sada zumunta da kuma bayyana abin da suka sani ko yadda ya shafi wani makusanci ko labarin da suka ji a kan yankin.

An jima dai ana zargin cewa ana hallaka mutane musamman bakar-fata a Cyprus ta Arewa, domin tun kafin labaran Ibrahim ya fito, an sha samun masu korafi dangane da zuwa karatu yankin.

A wasu lokutan kuma dalibai idan sun koma hutu ba sa sha’awar koma wa, wasu kuma kan yi korafin cewa suna shiga fuskantar barazana.

Yanzu dai abin da ke jan hankali shi ne tabbatar da adalci da bincike kan mutuwar Ibrahim Khaleel da kuma sauran dalibai irinsa da suka rasa rayukansu, ko wadanda rayuwarsu ke cikin barazana a kasahen ketare, kamar yadda ake bayyana wa a shafukan sada zumunta.

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

OBA OJIKU; Ya ce, GANI GA WANE -akwai dalibai da dama bakar-fata cikinsu har da ƴan Najeriya da suka yi mutuwar al’ajabi a Arewacin Cyprus a cikin ƴan shekarun baya-bayanan. Dan Allah ku zauna a gida ku yi karatu maimakon kokarin tafiya Cyprus.

Kauce wa Twitter, 2

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

Shima Senator Shehu Sani tsohon dan majalisa dattijai ya aike da gargadi da jan hankali ga iyaye kan su kare ‘ya’yansu sakamakon hadari da yanayin da duniya ta fada a ciki.

Kauce wa Twitter, 3

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

Ya ce; Mutuwar Ibrahim Bello Khaleel dan shekara 25 da sauran dalibai a arewacin Cyprus abin alla-wadai ne. Duniya na sake zama abin hadari, da kiyayya da rikici. Duk da cewa bamu tsira ba, ku ajiye yaranku a gida su yi karutun digirin farko zuwa lokacin da lamura zasu dawo daidai. Allah ya saka masa da gidan Aljanna.Amin

To sai dai yayin da ake gargadi ga iyaye kan su adana yaransu a gida wasu na ganin tabarbarewar ilimi a Najeriya ne ke taka rawa kuma yana daga cikin dalilan da ke tilastawa iyaye aike yaransu ƙasahen ƙetare don neman ilimi.

Kauce wa Twitter, 4

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 4

Ya ake dalibai suke mutuwa a Cyprus ta Arewa?

Babu dai wasu sahihin bayanai ko karin haske kan mutuwar dalibai ko mummunan halin da suke tsintar kansu a ciki a yankin.

Sai dai iyayen daya daga cikin dalibin daya rasa ransa na cewa mahukunta kasar na boye ainihin abin da ke sanadi mutuwar yara, kamar yadda aka gani akan Ibrahim.

Mahaifiyar Ibrahim, Hon. Justice Bello ta ce bayanan da jami’ar ta bayar kan mutuwar ɗanta sun ce kashe kansa ya yi, amma a cewarta babu wata alama da ke tabbatar da hakan.

Ta kuma zargi kasar cewa mai yiwuwa sun cire wasu sassan jikin ɗanta saboda gawar da aka kawo ya nuna kamar an farke cikin ɗanta sannan aka ɗinke daga baya.

Sannan ta shaida cewa kafin mutuwar Ibrahim sai da ya kirata a waya ya shaida cewa ta zo ta dauke shi daga wannan kasa idan ba haka ba za a hallaka shi.

Kauce wa Twitter, 5

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 5

Dalibai akalla dubu 120 daga sassa daban-daban na duniya ke zuwa kasar domin karatu.

Abin daya kamata a sani game da Cyprus ta Arewa

Ba amintacciyar kasa ba ce a duniya

Cyprus ta Arewa (wanda ake kira Jamhuriyar Turkiya ta Cyprus ta Arewa wato Turkish Republic of Northern Cyprus) yankin kasar Cyprus ne bayan mamayar da Turkiyya ta yi wa yankin a 1974.

Hakan na nufi Majalisar Dinkin Duniya da kasashen duniya ba sa kallonsa a matsayin kasa mai cikakken ‘yanci. Kasa guda da ta ke mata kallon kasa ita ce Turkiyya da ke juya akalarta.

Abike Dabiri Erewa ta ce ko Najeriya ba ta da alakar diflomasiya da ita.

A 1983 yankin ya ɓalle daga Cyprus

Al’ummar Cyprus ta Arewa, ko Cyprus ta Turkiyya sun bayyana kansu a matsayin ƙasa mai cin gashin kai a 1983, bayan shekaru 9 ana rikicin siyasa abin da ya kai ga dakarun Turkiyya su ka kai hari arewa a matsayin martani kan juyin mulkin soji da ‘yan ƙasar Girka suka shirya a wannan lokacin.

Amma ana tattauna ƙoƙarin hada kan yakin da kudancin Cyprus. Sannan shugabanta Mustafa Akinci ya alkawarta cimma yarjejeniyar zaman lafiya a lokacin zabensa a 2015.

Duniya na karɓar shaidar karatun makarantun Cyprus ta Arewa?

Duk da cewa kasar ba amintacciya ba ce a duniya, ana iya amfani da shaidar digirin kasar bayan tantacewa a matakin yankin da kuma kasar Turkiyya kafin ka iya amfani da shi.

Sannan wani abu da ke ƙwadaitawa dalibai zuwa karatu ƙasar shi ne arahar makarantu da kuma damar aiki a ƙasashen Turai.

Dalibai daga Afirka da Asiya na rige-rigen zuwa ƙasar karatu saboda damar samun sauki da kuma kafar da ƙasar ke bayarwa na samun aiki a Turai.

Yadda ake gina makarantu a ƙasar ya karu daga makaranta 6 a 2011 zuwa 30 a 2019.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...