Kar a yi saurin yanke wa gwamnatin Tinubu hukunci—in ji Yakubu Gowon

Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon, ya yi gargadin cewa kada a yi gaggawar yanke hukunci kan ayyukan gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Gowon ya bayyana haka ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa jiya bayan ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa.

Tsohon shugaban kasar ya ce ya shawarci Tinubu da kada ya damu da sukar da ake yi wa gwamnatinsa a halin yanzu.

Dattijon ya ce ya yi wuri a yanke hukunci a kan gwamnatin Tinubu.

Ya ce “To, ina gaya masa cewa babu wani shugaban Najeriya da zai iya kawo wannan matakin kuma bai samu dukkan rahotannin abin da ake fada a kansa ba.”

“Ina ganin gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance matsalolin kasar nan daban-daban.”

Wannnan zuwa ne a daidai lokacin da rayuwa ta yi ƙunci wa ƴan Najeriya yayin da farashin kayayyaki ke ci gaba da yin tashin gwauron zabi.

More from this stream

Recomended