Bangaren jam’iyyar New Nigeria People’s Party, da ta fi kusa da Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya gudanar da wani taro na kwamitin zartarwar jam’iyyar na kasa a Abuja, domin janye dakatarwar da aka yi wa tsohon ɗan takarar shugaban kasar.
Bangaren ya sanar da korar sabon shugaban riko na jam’iyyar na kasa, Manjo Agbo da wasu fitattun ‘ya’yan jam’iyyar da ke da ruwa da tsaki a dakatarwar Kwankwaso.
Matakin na zuwa ne sa’o’i bayan da kwamitin amintattu na jam’iyyar ya dakatar da Kwankwaso bisa zargin cin dunduniyar jam’iyyar.
An dauki matakin sanya wa Kwankwaso takunkumi tare da nada sabbin shugabannin kasa karkashin jagorancin Manjo kuma mukaddashin sakataren kasa, Ogini Olaposi da wasu mutane 18 a wani taron shugabannin jam’iyyar na ƙasa da aka yi a Legas da safiyar ranar Talata.