‘Kamar yau sallah nake ji da tarbar Sarkin Kano’

Wani mutum dauke da kwali mai rubutun nuna goyon baya ga Sarki Sanusi

Masu goya wa Muhammadu Sanusi na II baya sun yi masa gagarumar tarba, inda da dama suka yi ado da riguna da huluna dauke da sunan basaraken, yayin da wasu kuma suke kade-kade da raye-rayen maraba har ma da masu daga kwalaye dauke da rubuce-rubucen goyon baya.

Wani Bakano ya bayyana Sarki Muhammadu Sanusi na II, a matsayin jagora mai adalci da ya dukufa wajen share kukan talakawa, “hakan da muka ga ta bayyana a fili, shi ya sa dukkaninmu yanzu muke da goyon baya a kansa”.

Mutumin na daga cikin dubban Kanawan da suka fita don yi wa Sarki Sanusi maraba da yammacin ranar Lahadi, lokacin da ya koma gida bayan wata tafiya da ya yi, daidai lokacin da gwamnatin jihar ta rarraba masarautarsa zuwa gida biyar.

Image caption

Dafifin mutanen da suka tarbi Sarkin

Wakilin BBC Ibrahim Isah ya ce Sarki Sanusi ya sauka daga jirgin sama ne tun karfe hudu na yamma, amma bai isa gida ba sai karfe bakwai saboda yawan cincirindon da masu tarbarsa suka yi a titunan birnin Kano.

A cewarsa: “Duk da zafin ranar da ake yi, haka masoyan sarkin suka jure don yi masa kyakkyawar tarba.”

“Wannan tarba ce ta musamman. Muna farin ciki da dawowar sarkinmu. Mutum ne mai taimakon talaka, kuma duk abin da aka yi wa ‘ya mace abin na ransa,” in ji wata da ta je tarbar Sarki Sanusi.

Ta ce Allah Ya tsare musu shi, kuma “mu yanzu wa’annan kwanakin biyu ne ko zuwa uku da ya yi (ba ya nan), ji muke kamar ya shekara. Shi ya sa muka fito a matsayinmu na masoya (don) mu tarbe shi.”

Wata matashiya kuma ta fada wa BBC cewa ji take yi kamar yau sallah, “saboda yadda mutane suke ta farin ciki, suke ta nishadi. Ga shi dai azumi ake amma sarkin nan yadda ka san ba a taba ganinsa ba”.

Ibrahim ya ce sarkin bai gabatar da wani jawabi ba, kuma bai ce wa kowa uffan ba, lokacin da ya sauka daga motarsa ta alfarma ya shige gida.

Dawowar sarkin ta zo ne a ranar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya bai wasu daga cikin sabbin sarakuna na masarautun da ya kirkira sandunan girma, kwana guda bayan tabbatar da su a sarautu.

Sabbin sarakunan sun hada Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi da Dr Ibrahim Abubakar Sarkin Karaye da Alhaji Tafida Abubakar Ila Sarkin Rano da kuma Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya.

Matakin dai ya janyo gagarumar takaddama, inda wasu ke ganin a matsayin bi-ta-da-kulli saboda takun-sakar da ake zargin ya wanzu tsakaninsa da gwamnati, batun da Gwamna Ganduje ya musanta.

Ibrahim ya ce: “Duk da ikirarin da gwamnatin Kano ke yi cewa babu wani sabani tsakaninsu, (amma) babu wata shaida da ke nuna cewa ta gayyace shi zuwa taron (tabbatar da nadin sabbin sarakunan a ranar Asabar)”.

Gwamnatin jihar Kano dai ta ci gaba da sha’anin nadin sabbin sarakunan ne duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakata, har sai ta saurari wata kara da aka kai mata game da batun.

A cewar gwamnan su ba su ga wani umarnin kotu ba, har zuwa ranar da Asabar, sa’ar da ta gudanar da “taron nuna godiya” daga wadanda ya ba wa sarautun.

Gwamnatin Kano ta ce a shafukan sada zumunta kawai ta ji baun da ake yadawa game da umarnin babbar kotu, wanda kuma a cewarta bai isa hujja ba.

Image caption

Hanyar shiga gidan Sarki wato Kofar Kudu ta cika makil da mutane ‘yan tarbar Sarkin

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...