Kalli hotunan yadda zafi ya addabi nahiyar Turai

Wasu ma'aurata na sunbatar juna a gaban hasumiyar Eiffel

Hakkin mallakar hoto
AFP

—BBC Hausa

Image caption

Zafi ya sanya ‘yan yawon bude ido da jama’ar gari fita zuwa gaban hasumiyar Eiffel ranar Talata a birnin Paris na Faransa

Mutane da dama a fadin nahiyar Turai na kokarin kaucewa tsananin zafi da ake fama da shi a lokacin da yanayi ke kara hauhawa.

Yanayin wanda masana suka ce ka iya yin kisa – ya tsananta ne saboda iska mai zafi da ke fitowa daga yankin Sahara – kuma tuni ya sa aka soke jarabawar ‘yan makaranta a Faransa.

Sai dai masanan na hasashen yanayin zafin a kasashen Faransa da Jamus da Belgium zai iya kai wa matsayin da ba a taba gani ba a ‘yan kwanaki masu zuwa.

Masu yawon bude ido dauke da lema

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mutane na amfani da lema dan kare rana a birnin Roma

Wani mutum na tafiya, ya yin da wasu mata ke daukar hoton dauki da kanka

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Can a birnin Nice na Faransa, tsananin zafi ya kai maki 33 a ma’aunin selshiyos a ranar Litinin

Yara na shiga tafkin Geneva

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Yara sun yi amfani da wannan damar dan shiga tafkin Geneva a kasar Switzerland

Matasa na fadawa ruwa

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Zafin da ake yi ya sanya matasa na kundunbala a Birnin Copenhagen, da ke Denmark

Yara na wasa a ruwa

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wannan hoton wani yaro ne da ya ke wasa a wani karamin kududdufi da baya gudu a birnin Reins a kasar Faransa

Yara ne ke kasan wani tsauni da ke zubo da ruwa

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Birnin Madrid na Sifaniya kuwa, dole yara suka tsaya kasan wani tsauni da ke zubo da ruwa saboda zafi

Dabbobi ma su na jin tsananin zafin

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wani ma’aikacin gidan namun daji ke Birnin Berlin na kasar Jamus ke fesawa wata Giwa ruwa da mesa dan rage mata zafin da ta ke ji

Mutane na tuka kwale-kwale

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wasu mutane ke tuka kananan jiragen ruwa a tekun Danube na birnin Vienna a kasar Austria

Wata mace na motsa jiki

Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Sai dai birnin Landan yanayi mai dadi ake yi inda rana ta dan fito kadan, saboda makwannin da suka wuce an yi ruwa mai hade da iska. Amma duk da haka wasu na dakon fitowar rana a kwanaki masu zuwa

Duka hotunan na da hakkin mallaka

More from this stream

Recomended