Juyin mulki:Yawan manyan sojoji da aka kama ya karu zuwa 42

Yawan sojojin da aka kama kan zargin shirya yiwa gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin mulki ya karu ya zuwa 42.

Tun da farko hedkwatar tsaron Najeriya ta sanar da kama manyan sojoji 16 kan zargin rashin biyayya da bata alakanta ba da juyin mulki.

Amma kuma wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kama su ne kan zargin yunkurin da su ka yi na kawo ƙarshen shekaru 26 da Najeriya ta yi kan turbar dimakwara

Wasu majiyoyin jami’an tsaro sun fadawa jaridar Daily Trust cewa yanzu haka manyan jami’an na cigaba da fuskantar tambayoyi domin gano hannun da su ke da shi kuma zurfin shirin da ake zargin su shiryawa

” Ya zuwa yanzu an kama manyan jami’ai 42 ana cigaba da yi musu tambayoyi domin gano hannun da su ke da shi da kuma gano cewa ko akwai cikakken shiri a kasa ba wai kawai tattauna batun su ka yi ba a baki,” a cewar majiyar.

Wata majiyar ta bayyana cewa yawan mutanen na iya karuwa a yayin da sashen DIA na  tattara bayanan sirri na rundunar tsaro ke cigaba da bin diddigi musayar maganganu da kuma yiyuwar ko akwai wadanda suka dauki nauyin samar da kudin aiwatar da juyin mulkin.

More from this stream

Recomended