Juyin mulki:Amurka ta dakatar da tallafin dala miliyan $200 da take bawa Niger

Gwamnatin Amurka ta dakatar da tallafin kusan dala miliyan 200 da take bawa ƙasar Nijar.

Dakatar da tallafin ya yi dai-dai da sashe na 7008 kasafin kuɗin shekara na ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

Hakan na zuwa ne biyo bayan jerin takunkumi iri-iri da aka ƙaƙabawa kasar tun bayan da sojoji suka hamɓarar da gwamnatin shugaban kasa, Mohamed Bazoum.

A wata sanarwa ranar Talata, Matthew Miller mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya tabbatarwa da ƴan kasar ta Nijer cewa za su cigaba da amfana da tallafin ayyukan jin kai daga Amurka da ya shafi abinci da kuma sashen kiwon lafiya.

Amurka ta kuma nanata kiranta na sakin tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum tare da iyalinsa da kuma dukkan mutanen da ake tsare da su.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da...

Sojoji a birnin Ibadan  sun kama ƴan fafutukar kafa ƙasar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Masu fafutukar sanye da...