Juventus na son sayar da Ramsey, Barcelona ba za ta sayar da Fati ba

Aaron Ramsey

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Juventus tana shirin sayar da Aaron Ramsey shekara daya kacal bayan ta sayo shi daga Arsenal a yayin da take son yin tsimin £400,000 duk mako, kuma ana sa ran dan wasan na Wales mai shekara 29 zai koma Manchester United. (Mail)

Daraktan Barcelona Xavier Vilajoana ya karyata rahotannin da ke cewa kungiyar ta tattauna da Manchester United game da sayar da Ansu Fati, yana mai cewa dan wasan na Spaniya mai shekara 17 ba na sayarwa ba ne. (Sport)

Watakila Leicester City ta rage farashin da ta sanya a kan dan wasan Ingila mai shekara 23 Ben Chilwell tun da ya bayyana aniyarsa ta komawa Chelsea. (Evening Standard)

Dan wasan Portugal Cedric Soares, mai shekara 28, zai iya barin Arsenal ba tare da ya buga mata wasa ko daya ba tun da ya koma kungiyar daga Southampton a watan Janairu. (Goal)

Everton tana jiran Nice ta taya dan wasanta mai shekara 30 Morgan Schneiderlin, amma akwai yiwuwar za su yi asarar £17m kan dan wasan na Faransa wanda suka sayo daga Manchester United. (Mail)

Tsohon dan wasan Jamus da Liverpool Dietmar Hamann ya bai wa dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz, mai shekara 21, shawara kada ya amince da tayin komawa Manchester United yana mai cewa gara ya koma Chelsea. (Mirror)

Dan wasan Real Madrid da Spaniya mai shekara 34 Sergio Ramos “ya yi mafarkin” cewa zai ci gaba da buga tamaula a Bernabeu har lokacin da zai yi ritaya duk da cewa ba a yi masa tayin sabunta kwangilarsa ba wacce za ta kare a bazara mai zuwa. (Marca)

Mahaifin dan wasan Burnley Dwight McNeil, mai shekara 20, ya bukaci da kada ya koma Manchester United ko Leicester City inda ya umarce shi ya ci gaba da zama a Clarets. (Sun)

Real Madrid tana son dauko dan wasan Faransa mai shekara 29 N’Golo Kante daga Chelsea inda za ta biya shi £71m. (AS – in Spanish)

More News

Peter Obi Ya Ziyarci Mutanen Da Su Ka Ƙone Sakamakon Wutar Da Wani Ya Cinnawa   Masallaci A Kano

Ɗan takarar shugaban ƙasa  a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam'iyar Labour Party (LP) Peter Obi ya ziyarci mutanen da wani matashi ya cinnawa wuta a...

An sanar da zaman makoki na kwana biyar saboda mutuwar shugaban kasa a Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi...

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...