Jordan na haɗa kai da Masar kan shirin sake gina Gaza

Firaministan Jordan, Jafar Hassan, ya bayyana cewa ba wanda zai iya raba Falasɗinawa da Gaza.

Ya ce ganawar da Sarki Abdullah na Jordan ya yi da Shugaban Amurka, Donald Trump, a jiya ta jaddada matsayin Jordan na tallafa wa shirin sake gina Gaza, tare da tabbatar da cewa Falasɗinawa ba za su bar yankin ba.

“Jordan na aiki tare da Masar da Falasɗinu domin fitar da daftarin sake gina Gaza,” in ji shi.

A baya mun ruwaito cewa Masar ita ma ta ce za ta gabatar da “cikakken kundin” sake gina Gaza.

More from this stream

Recomended