
Gwamnatin tarayya ta ce tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na nan kalau kuma ya fice daga ƙasar Guinea Bissau bayan da sojoji suka yi juyin mulki a kasar.
A wata sanarwa ranar Alhamis, Kimiebi Ebienfa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ya ce Jonathan ya bar kasar ta Guinea Bissau a wani jirgin na musamman tare da yan tawagarsa.
“Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya na nan kalau cikin lafiya kuma ya fice daga ƙasar Guinea Bissau. Ya bar kasar a cikin wani jirgi na musamman tare da yan tawagarsa ciki har da Muhammad ibn Chambas,” a cewar Ebienfa a cikin sanarwar da ya fitar.
Tsohon shugaban kasar yaje kasar ne domin sanya idanu a zaɓen shugaban kasar da aka gudanar.
A ranar Laraba ne sojoji suka sanar da karɓe Mulki a kasar dai-dai lokacin da ake dakon sakamakon zaɓen shugaban kasar da aka gudanar.

