John Cena Ya Yi Ritaya Daga WWE Bayan Shekaru 24

Fitaccen ɗan kokawa John Cena ya ajiye takalmin kokawa bayan shafe shekaru 24 a WWE.

Ya yi wasan bankwana a birnin Washington, inda Gunther ya kayar da shi ta hanyar tilasta masa mika wuya.

Bayan fafatawar, Cena ya bar takalmi da abin ɗaure hannu a cikin zoben karawa, alamar ritaya, sannan ya yi bankwana da masoya.

Cena na barin WWE a matsayin zakaran duniya sau 17 kuma ɗaya daga cikin manyan jaruman kokawa a tarihi.

More from this stream

Recomended