Jirgin sojan saman Najeriya ya sake kashe fararen hula a jihar Neja

Akalla fararen hula biyu aka ruwaito an kashe bayan da wani jirgin yaki ya bude wuta kan jama’ar gari a kauyen Kurgi dake karamar hukumar Mariga ta jihar Niger.

Lamarin marar dadin ji da ya faru a ranar Juma’a 25 ga watan Janairu ya kuma jikkata mutane da dama.

Wani rahoto da wata ƙungiya ta fitar ya bayyana cewa sai da jirgin ya rika shawagi kafin daga bisani ya yi ruwan wuta kan mutanen.

Harin jirgin saman yakin wani ɓangare  na zafafa farmakin da aka ƙaddamar a  jihohin Neja da  Kwara ranar 20 ga watan Janairu a matsayin martani kan karuwar ayyukan yan ta’adda a arewacin jihar a cikin yan watannin  nan.

Da take mayar da martani kan faruwar lamarin Rundunar Sojan Saman Najeriya ta ce ta  lura da zargin da aka yi na kisan fararen hula bayan farmakin da ta kai kauyen Kurigi .

A wata sanarwa mai dauke da sahannun Ehiomem Ejedame  dake magana da yawun rundunar ya bayyana cewa  rundunar ta na sane nauyin rahoton asarar rayuka da raunuka da aka samu a harin.

Rundunar ta kuma bayyana matukar da damuwarta da alhinin mutanen da abun ya rutsa  da su kana ta ci alwashin gudanar da cikakken bincike kan harin.aonoj

More from this stream

Recomended