Jirgin Saman Sojan Najeriya Ya Faɗo A Kaduna

Wasu matuƙan jirgi biyu na rundunar sojan saman Najeriya sun tsira da ransu bayan da jirgin da suke ciki ya faɗi a lokacin da suke samun horo a ranar Alhamis.

A cewar, Edward Gabkwet Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar Sojan Saman Najeriya lamarin ya faru ne da tazarar nisan mil 3.5  daga filin jirgin saman soja dake Kaduna.

Ya ce jirgin na horar da sojoji ƙirar Super Mushshak ya samu ƴar ƙaramar matsala da tasa ya fado da misalin ƙarfe 2:35 na ranar Alhamis.

Gabkwet ya ce dukkanin matuƙa jirgin biyu sun kubuta ba tare da samu wani mummunan rauni ba.

Tuni shugaban rundunar sojan saman Najeriya, Air Marshal Hassan Abubakar ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan faruwar lamarin

More from this stream

Recomended