Wani jirgin fasinja mai dauke da fasinjoji 181 ya yi hatsari a birnin Muan, Koriya ta Kudu, ranar Lahadi, yayin da ya fuskanci matsaloli a tayun saukarsa.
Jirgin kamfanin Jeju Air, wanda ke dauke da fasinjoji 175 da ma’aikata shida, ya kauce daga hanyar saukarsa, ya bugi shinge, sannan ya kama da wuta a filin jirgin saman Muan, bayan ya tashi daga Bangkok, Thailand.
Rahoton AP News ya tabbatar da cewa wasu kafafen watsa labarai na Koriya ta Kudu sun bayyana cewa wutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 28, yayin da aka samu ceto na mutum biyu.
Sai dai daga baya wasu rahotanni sun nuna cewa adadin waɗanda suka mutu ya haura 100.