Jirgin kasa ya markade shanu 50 a jihar Kaduna

Akalla shanu 50 ne a jiya jirgin kasa dake kan hanyarsa ta zuwa Abuja ya markade su har lahira, Kwamishinan ƴansandan jihar Kaduna, Ahmad Abdulrahman shine ya bayyana haka jiya.

Ya ce rundunar ta samu kiran kai daukin gaggawa akan hatsarin da misalin 11:45 na safe inda ya kara da cewa shi da kansa ya jagoranci manyan jami’an rundunar ya zuwa wurin da abin yafaru dake Kasarami a gundumar Jere karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

“Lokacin da muka isa wurin mun gano cewa ba kamar yadda rahotannin farko ke cewa harin yan ta’adda ne, gaskiyar abinda yafaru hatsari ne,”kwamishinan ya ce.

A cewarsa wasu fulani da suka kwana a Kasarami sun tambaya ko za su iya tsallakawa da shanunsu amma aka ba su gurguwar shawara cewa jirgi baya wucewa ranar Lahadi.

” A daidai lokacin da suke tsallakawa ne takan digar jirgin sai jirgi mai gudu daga tashar Rigasa akan hanyarsa ta zuwa Abuja ya nufi wurin da suke tsallakawa ya kuma markade shanu 52 har lahira.”

Ya ce an bayar da umarnin yanka shanu 27 da suke da rai inda aka sayar da su domin rage asara.

Fulanin na kan hanyarsu ne ta zuwa jihar Katsina.

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...