Jirgin fasinja na Air Niugini ya fada a teku kusa da Micronesia

Small boats surround the Air Niugini plane in the water

Hakkin mallakar hoto
James Yaingeluo

Wani jirgin fasinja ya fado daga sama a teku kusa da filin jirgin sama na Chuuk International Airport na Micronesia bayan da ya kasa sauka.

Hotunan jirgin sun rika zagayawa a shafukan sada zumunta daga Papua New Guinea, inda suka nuna jirgin yana zaune cikin ruwa kusa da gabar teku.

Amma babu wanda aya sami rauni cikin fasinjoji 35 da ma’aikatan jirgin 12 a jirgin mai lamba ANG73.

Ba a san dalilin da ya janyo wannan hatsarin ba, amma ana sa ran za a gudanar da bincike nan ba da dadewa ba.

Manajan filin jirgin sama na Chuuk, Jimmy Emilio ya sanar da BBC cewa jirgin ya fada cikin teku kimanin yadi 160 daga titin filin jirgin saman.

Manajan ya ce, “An tafi da wadanda ke cikin jirgin mai samfurin Boeing 737-800 zuwa asibiti kuma an duba su, inda aka tabbatar dukkansu na cikin koshin lafiya.”

Jirgin ya taso ne daga tsibirin Pohnpei na Micronesia zuwa Port Moresby, babban birnin Papua New Guinea, amma ya tsaya a tsibirin Weno akan hanyarsa.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...