
Fasinjoji da dama ne suka yi carkwo-carkwo bayan da jirgin ƙasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga kan digarsa a tashar Asha dake birnin tarayya Abuja.
Ɗaya daga cikin fasinjojin dake cikin jirgin ya faɗawa jaridar The Cable cewa jirgin ya kauce daga kan digarsa ne da misalin ƙarfe 03:30 na rana ƙasa da mintuna 30 bayan da ya bar tashar Kubwa.
“Fasinjoji sun yi carkwo-carkwo suna zaman jira kuma babu alamun zuwan hukumomi da aka sanarwa da faruwar lamarin,”
Wannan ne karon na biyu cikin makonni biyu da jirgin ƙasar ya ke sauka daga kan layinsa.
A ranar 26 ga watan Mayu jirgin ya kauce daga kan layinsa bayan da ya baro tashar Rigasa dake Kaduna akan hanyarsa ta zuwa Abuja.
Tarago uku ne ya sauka daga kan digar jirgin amma babu mutanen da suka jikkata.