Jihar Ogun za ta riƙa biyan ₦77,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya amince a riƙa biyan ₦77,000 a matsayin mafi girma ƙarancin albashi a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Tokunbo Tlabi ya ce fara biyan mafi ƙarancin albashin zai fara aiki ne nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Talabi na magana ne bayan wata ganawa da shugabancin kungiyar ƙwadago ta NLC da TUC da kwamitin tattaunawa na haɗin gwiwa JNC.

Ya ce an kira taron ne bisa umarnin gwamnan wanda ya bada umarnin cewa kada a riƙa biyan wani ma’aikaci a jihar ƙasa da ₦77,000 farawa  daga watan Oktoba.

Talabi ya ƙara da cewa gwamnan ya umarci kamfanoni masu zaman kansu da su tattauna da masu ruwa da tsaki domin fitar da matsaya kan mafi ƙarancin albashin da za su riƙa biyan ma’aikatansu.

Ya ce gwamnati za ta kafa kwamitin sanya idanu da zai tabbatar da kamfanoni masu zaman kansu sun fara biyan mafi ƙarancin albashin.

Related Articles