Jihar Niger Za Ta Karfafa Matakan Tsaron A Lokacin Bukukuwan Sallar Layya.

[ad_1]

Biyo bayan ganawar da Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi da jami’an tsaro da sarakuna, rundunar ‘yan sandan jihar ta ce za ta girke ‘yan sanda 2,030 a wurare daban cikin jihar, domin tabbatar da an gudanar da bukuwan sallah lami lafiya.

DSP Abubakar Dan Inna, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar,ya ce zasu maida hankali ne a wuraren da suke ganin akwai bata gari a cikin bayanin da ya yiwa Sashen Hausa.

Shi ma kakakin gwamnan jihar Jibril Baba Ndagi, ya tabbatar da zaman shawarwari da gwamnan da jami’an tsaro da kuma sarakunan gargajiya dake jihar suka yi.

Sai dai al’ummar yankin Sarkin Pawa, da Shiroro masu iyaka da jihar Kaduna, suna ci gaba da fargaba akan janye jami’an tsaro da aka yi a yankin nasu duk da cewa suna fama da masu garkuwa da mutane suna karban kudin fansa.

Alhaji Adamu Erana, wani dan siyasa a yankin yayi kiran da adawo da jami’an tsaron da aka kwashe daga yankin. A cewarsa masu garkuwa da mutane suna ci gaba da satar mutane kuma sai an ba da kudi su sako su.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari

[ad_2]

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...