Jihar Neja za ta riƙa biyan  ₦80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya amince a riƙa biyan ₦80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar.

Gwamnan ya amince da fara biyan kuɗin a matsayin mafi ƙarancin albashi a ranar Juma’a  a yayin wani taron ganawa da wakilan ƙungiyar kwadago ta jihar a Minna babban birnin jihar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Bago ya ce jihar ta Neja ta amince ta fara biyan mafi ƙarancin albashi.

A ƴan kwanakin nan dai ana ta cigaba da samun ƙarin jihohi da suke tabbatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin da gwamnatin tarayya da kuma ƙungiyar ƙwadago suka amince da shi.

More from this stream

Recomended