Wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya sun fara neman afuwar ‘yan kasar a kan da su yi hakuri dangane da yanayin kunci da kasar take ciki yanzu haka sakamakon wasu matakai da gwamnatin kasar ke dauka da manufar gyara.
Daya daga cikin jigo a jam’iyyar Farouk Adamu Aliyu, a cikin wata hira da ya yi da BBC, ya ce jama’a su yi hakuri da halin da ake ciki na matsi wanda ya ce dalilai ne suka haddasa hakan.
Farouk Adamu Aliyu ya ce,”Ni ma a iya sanina bana zaton an taba shiga kunci irin wannan na yanzu, kamar a bangaren abinci gaskiya ne an samu matsalar hahhawar farashi da dai sauransu”.
Ya ce, abubuwa da dama ne suka kawo hakan, sannan kuma ya ce mutane da dama an sha kiransa ana masa Allah ya isa saboda yadda rayuwa ta yi kunci a yanzu.
Jigo a jam’iyyar ta APC ya ce,” Ga wadanda suke da sanin tallafa mana da wani abu a lokacin da muke yakin neman zaben shugaba Buhari musamman a shekarar 2015, to muna neman suyi mana gafara”.
Farouk Adamu Aliyu, ya ce ba yana bayar da wannan hakuri ne don wani abu ko kuma yana nadama a kan ja gaban da suka yi wajen ganin shugaba Buharin ya samu nasara a zaben, sam ko kadan baya nadama inji sa.
Ya ce, ya bayar da wannan hakuri ne domin ba yadda zaka yi ka daki mutum sannan ka hana shi kuka.
“Ina so na ja hankalin talakawan Najeriya a kan suyi la’akari da cewa mu masu hannu da shuni da dan APC da dan PDP, uwarmu daya ubanmu daya”.
A jam’iyance suna APC da PDP ba bu bambanci, bambancin kawai shi ne jagoranci.
“Mu da muke tare da Buhari, misali ni Farouk Adamu Aliyu wallahi duk randa na samu labari kan cewa za a zauna da shugaba domin ayi wani abu na algus, wallahi tallahi zan rabu dashi”.
To amma wallahi ba ya yi, don haka mu masu hannu da shuni mune muke yaudarar talakawan Najeriya, don haka yakamata talakawan Najeriya su gane wannan inji Farouk Adamu Aliyu.
Ya ce ya kamata talakawa su gane idan har an zo zabe zaka iya yin jam’iyyarka, amma idan har kana gani jam’iyyarka bata tsayar da wanda ya dace ba to ka zabi wanda kake gani zai kai ka.