Daraktan Gudanarwa na Progressive Governors Forum (PGF), Folorunso Aluko, ya bayyana cewa nan da shekarar 2027 jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta karɓi gwamnonin wasu jihohi guda shida, wanda hakan zai kai adadin jihohin da jam’iyyar ke mulki zuwa 30.
Aluko ya yi wannan bayani ne a taron dabarun aiki na kwata-kwata na ma’aikatan yada labarai daga jihohin da APC ke mulki, wanda aka gudanar a Maiduguri, jihar Borno, a ranar Alhamis.
Ya ce jam’iyyar APC tana kan kyakkyawan matsayi wajen cimma burinta da kuma ƙarfafa matsayinta na dabarun siyasa a fadin ƙasar.
Aluko ya bayyana cikakken tabbacin cewa Progressive Governors Forum za ta bunƙasa daga jihohi 24 zuwa aƙalla 30 kafin ƙarshen shekarar 2027.
A cewarsa, yana da muhimmanci gwamnoni da gwamnati a matakin jihohi su daidaita manufofinsu da hangen nesa na gwamnatin tarayya, tare da yin aiki cikin gaskiya da haɗin kai domin gina ƙasa mai ɗorewa.
Aluko ya ce, “Da ikon Allah da yardar ‘yan Najeriya, muna da tabbacin cewa PGF za ta tashi daga jihohi 24 na yanzu zuwa aƙalla jihohi 30 kafin ƙarshen shekarar 2027.
“Muna ƙarfafa tsararin dabarunmu kuma muna daidaita saƙonninmu da auna tasirinsu.
“Kuma yayin da muke kallon shekarar 2027, imaninmu yana nan daram. APC za ta ƙara ƙarfi,” in ji shi.
Jam’iyyar APC Ta Ce Za Ta Mallake Jihohi 30 Kafin Ƙarshen Shekarar 2027

